AL UMMAR GARIN KUCHERI SUN YI KIRA GA GWAMNATI DA TA KAWO MASU DAUKI NA JAMI'AN TSARO
Daga Gambo Abubakar Kaduna
Al umar garin Kucheri da ke a Karamar hukumar Tsafe ta Jahar Zamfara, sun yi kira ga Gwamnatin Jahar karkashin jagoranci Gwamna Dauda Lawal da a Samar ma su da sansanin jamian tsaro don kare rayuwa da dukiya daga ta addancin yan bindiga da ke barazana ga rayuwar jama'ar garin.
Wannan kira ya zama wajibi ganin yadda yan ta'addan su ka azabci mutanen garin da farmaki a kowane lokaci, don daukar mutanen kauyen da kuma baki matafiya a kowane lokaci.
Wani mazauni kuma Dan asalin Kucheri Wanda ya nemi a sakaya sunan shi, ya kara da cewa a kusan killum yan bindigan kan fito ko ta gabas ko yamma akan babura, sukan bude wuta ga duk Wanda su ka gani, idan kuma rufci mota za ta wuce su kan amfani da wannan damar don bude mata wuta idan ba ta tsayaba.
Irin wannan ya faru kwanan nan a ranar alhamis da misalin karfe sha biyuvna rana, inda su kai awan gaba da wata matar Aure a tsakiyar garin, kafin faruwar haka kusan kullum sai sun bude ma mutanen garin da motacin matafiya wuta.
Wani Dan kasuwa mazaunin garin Kucherin Wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa yayi bayanin cewa abun bakin ciki shine duk da wannan hali da mutanen garin ke ciki.
Sai gashi a kwanakin baya jamian tsaro sun zo sun yi awan gaba da jama'ar garin wadanda ba su ji basu gani ba, sama da mutum Hamsin wai bisa zargin da hannunsu wajen kashe wani manajan banki da yan ta'addan su ka harba a gefen garin.
Duk da an sakesu a ranar bayan an gano mutanen kirkine ba bata gariba, al'amarin ya sosa rayuwar mutane da dama, kasancewar mutanen garin musamman matasa ba ci ma kwance ba ne, sun yi suna wajen neman na kai tun asali.
Akan haka mu ke kira ga wannan gwamnatin mai adalci ta da duba mamu, don Samar da jamian tsaro a garin nan mai albarka, ko ba komi gwamnatin mu ce don garin Kucheri na cikin garin da su ka taka rawa wajen zaben gwamnatin nan a zaben da ya gabata.
Ya kara da cewa yan ta'addan na shigowa ta kowace mashiga a kowane lokaci, wannan ya faru ne don ganin ba mu da jami'in Tsaro ko guda, sabanin makwabtan mu garin wanzamai.
Comments
Post a Comment