Jam'iyar ADC Na Neman Jama'a A Shekarun Baya, Amma Yanzu Jama'a Ke Neman ta, Inji Shugaban ADCn Tsafe



Daga Gambo Abubakar Kaduna

Shugaban Jam'iyar ADC a karamar  hukumar Tsafe Jahar Zamfara, Alhaji Mustafa Kabir Tsafe, ya bayyana cewa a da Jam'iyar ADC ta kasance tana neman Jama'a da su shigo don raya Jam'iyar,  amma halin yanzu mutane  ne ke tururuwa don neman ta da shugabannin ta.

  Jamiyar ADC ta samu tagomashin ne a sanadiyar hadakar da ta shiga tare da wasu jam'iyu, wanda a yanzu ta kasance Jam'iyar adawa ta farko da gwamnatin APC ke shakka.

 Alhaji Kabir Mustafa ya kara da cewa, duba kaga  kyakkyawar shugabancin  na kasa a karkashin David Mark Da sakatarenta Abdul razak Abesola, mutane ne jajartattatu kuma ma su akida da kima a kasar nan.

 Jamiyar ADC da ma ta na da shugabanci tun farkon kafuwarta a shekarar 1999 lokacin gama garin zabe, a wannan lokacin an inganta tsarin Jam'iyar ne kawai yadda zai yi dai dai da wannan karni, don kawar da matsalolin rashin tsaro, yunwa da cin hanci da rashawa da yayi katutu a kasa.

"Na samu kiran waya da sallama  a gidana daga mutane daban daban yan siyasa da wadanada ba yan siyasa ba don neman sanin hanyoyim da ka'idojin shiga Jam'iyar ta mu mai albarka.".

Akan haka ne shugaban ke kira ga jamaa da su kwantar da hankalinsu ADC a shirye ta ke da tafi da kowa, a kowane matsayi da suke da shi, musamman matasa, wadanda su ne kashin ba yan Jama'a, kuma yan gwagwarmaya ceton al'uma.

 Shima a na shi zan tawa da manema labarai Comrade Aliyu Sani, kuma tsohon Dantakarar Danmajalisar dokoki ta tarayya mai wakiltar Tsafe Gusau, a zaben da ya gabata,  Jam'iyar ADC jam'iyace ta hadaka don tsamar da kasa daga matsaloli na shugabanci.

 Bambancin Jamiyar ADC da wasu jam'iyu, shine kuduri da kasancewa jamiyar ce ta matasa, wadanda ke shirye don fidda kasar nan akan matsalar shugabanci na gari da kasar nan ke fuskanta, da ciyar da kasa gaba.

Yayi kira ga shugabanni da yan yan Jam'iyar ADC da su yi hakuri wajen tattalin baki, da buda hannayensu, don tarbar baki ma su  shigowa wannan Jam'iyar, kuma muna da tabbacin tasirin wannan gwagwarmaya.

Comments

Popular posts from this blog

Zamfara FRSC Gets New Sector Commander

Zamfara Health Commissioner Resolves NMA Leadership Tussle, As She Receives Elders Commendation

Tsafe Development Forum Appeals For An Urgent Support To The Victims Of Bandits Attacks In Chediya Ward