APC Malamiyya Akida Sun Kai Ziyara Goyon Baya Ga Katukan Tsafe


Daga Gambo Abubakar Kaduna

 Tsohon Shugaban Ma’aikata a fadar Gwamnatin Jihar Zamfara a lokacin mulkin Gwamna Abdul azeez Abubakar Yari, Injiniya Abdullahi Abdulkarim, Katukan Tsafe, ya karɓi ziyarar shugabannin Ƙungiyar Malamiyya Aƙida ta Jihar Zamfara.

Taron wanda ya gudana a ofishinsa dake Unguwar Marafa da ke Kaduna, a karkashin shugaban kungiyar na jaha Alhaji Murtala Mai Tsafe.

 A nasa jawabin Katukan Tsafe, Ya ya yi maraba da murna da wannan ziyara ta su, kuma ya bayyana cewa ya karɓe su ne a madadin Jagora Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar (Marafan Sokoto) da amininsa Ministan Tsaron Ƙasa, Hon. Bello Muhammad (Matawallen Maradun).

 Tsohon Kwamishinan ruwa ya kara da cewa, jam'iyar APC a shirye take ta tafi da kowa don samun nasarar Jam'iyar a zabe mai zuwa, musamman la'akari da wannan kungiya ta Malamiya Akida wacce ke dauke da tarihin wani jajirtaccen Dan siyasa,(Malami Yandoto).

 Injiniya Abdulkarim har ila yau ya sha alwashin mika sakonsu ga jagororin jamiyar, tare da bada tabbacin yin aiki kafada kafada don ci gaban jama'ar jahar zamfara da ma kasa baki daya.

 Tun farko a nasa jawabin Shugaban ƙungiyar na jiha, Hon. Alh. Murtala Mai Tsafe, ya bayyana cewa sun kai wannan ziyara ne domin sabunta mubayi’arsu da nuna goyon baya ga Jagora da Amininsa a madadin dukkan mambobin ƙungiyar a fadin jihar Zamfara.

 Ya kara da cewa shugabanni da memboba na wannan kungiya na goyon bayan kudirin da kiraye kirayen da jama' a keyi don yin takararsa na Sanata a zamfara  ta Tsakiya.

 "Wadanda su ka halarci ziyarar sun hada da shugabanni daga kananan hukumomin Bungudu, Gusau, Maru da kuma Tsafe.'

Comments

Popular posts from this blog

Zamfara Health Commissioner Resolves NMA Leadership Tussle, As She Receives Elders Commendation

Tsafe Development Forum Appeals For An Urgent Support To The Victims Of Bandits Attacks In Chediya Ward

Zamfara Health Ministry, Ministry Of Agriculture, WHO, Collaborate To Prevent Outbreak Of Anthrax In The State