Samun Irinsu Abdual azeez Yari Da Katuka A Cikin Al'Umma, Alama ce Allah Na Son Jama'ar Da Rahama:- Malam Sani Liman
Daga Gambo Abubakar Kaduna
Shahararran Malamin addinin musulunci a Jahar Zamfara Sheickh Sani Liman Tsafe ya bayyana cewa "samun mutane Irin su Sanata Abdul'azeez Yari Abubakar Marafan Sakkwato da Yaransa Injiniya Abdullahi Abdulkarim Katukan Tsafe, a cikin Al'Umma alama ce ta nunin Allah ya albarkacesu Jama'ar da rahama.
Bisa ganin jajircewarsu wajen tallafawa, da taimakon Al'Umma da yi ma addini hidima, a kowanne lokacin ba tare da gajiya wa ba, ga jama'ar yankin su na Tsafe da Jahar Zamfara da kuma kasa baki daya.
Malam Sani Liman ya yi wannan bayanine a lokacin ziyarar gani da ido da ya kai a katafaran masallacin da Katukan Tsafe ya gina, a unguwar Marafa Estate da ke grain Kaduna.
Shahararran Malamin addinin musulunci ya kara da cewa, Alqur'ani ya yi bayyana cewar Masu imani kadai ke iya gina Masallaci su Kyautata shi da kuma raya shi da ibada.
"Hadisin manzon Allah Muhammad SAW yace, duk mutumin da ya gina Masallaci don Allah da yardarsa, Shi kuma Allah yai alkawalin zai gina ma shi Daki a cikin Aljanna."
Shi ma a nasa jawabi a kwatankwacin ziyara, shugaban majalisar malamai ta jama atul izalatul bid'ah wa ikamatus Sunnah, Sheikh Khalil Mustafa Dunfawa, ya yi kira ga ma su kudi da Yan siyasa da su yi koyi da aiyukan alheri da Katukan Tsafe keyi tare da maigidansa Marafan Sakkwato.
Ta wajen ciyar da Al'Umma da abinci, da taimakon addini, ta bangaren Da 'awa da gina Masallaci da makarantu, bai tsayanan, har taimakon marassa lafiya da gajiyayyu a cikin Al'Umma.
Akan haka ne muke kira ga Jama'ar Tsafe, da Jahar Zamfara da kasa baki daya da su taimaka mashi da addua don neman kariya daga shedan, da fatar samun lada cikakkiya daga Allah.
'Al ummar wannan yankin tabbas Allah Subhanahu waya'ala, ya arzurtasu da rahamarsa, ganin yadda talauci yayi katutu a sakamakon annobar Yan bindiga, sai gashi wadannan sun bayin Allah sun jajirce wajen taimakon Al'Ummarsu, wannan abun sha awane.
Comments
Post a Comment