ANYI KIRA GA AL'UMMA DA SU DUKUFA DA ADDU'A A CIKIN WATAN RAMADAN DON NEMAN MAFITA GA ALLAH, AKAN MATSALAR RASHIN TSARO
Daga Gambo Abubakar Kaduna
Matashin dan Kasuwa a karamar hukumar Tsafe da ke Jahar Zamfara, Alhaji Isah Ali Yankuzo, ya yi kira ga jama'ar musulmi da su dukufa wajen yin addu'a ga Allah da ya ya ye mana masifar tsaron da ta addabi yankin da Jahar Zamfara.
Musamman a cikin wannan wata mai alfarma wanda Allah ke amsar bukatun bayinsa.
Alhaji Isah Ali Na Yankuzo, har ila yau yai kira ga Jama'a musamman ma su hannu da Shuni da su tallafawa jama a wajen ganin sun yi Azumi cikin walwala da kwanciyar hankalin.
"Ma fi yawon Jama'a na dogara ga Yan siyasa kawai wajen taimakon Al'Umma, taimako ya rataya ga duk mai abunda zai iya badawa ga wanda ke bukata don ganin ya yaye mashi damuwa, komin karanchinta."
Matashin dan Siyasa ya kara da cewa,addua itace Makamin mumini da dogaro ga duk wata masifar da yake fuskanta, da yin yakinin Allah zai yaye ko wace irin masifa ce.
"Alumma da ya wa na cikin Kunchi a dalilin Yan bindiga da kuma fashin samun damar yin noma don gudanar da lalurorinsu na yau da kullum."
Honarabul Isah, har ila yau ya na taya Al'Ummar musulmi na duniya murnar riskar wannan wata, da fatar Allah ya sa a dace da ladan da ke cikin wannan watan mai alfarma.
"Ina kuma yin addu'a ga musulmin da su ka rasa rayuwar su a sakamakon annobar Yan bindiga da Allah ya anshi shahadarsu, wadanda su ka rasa dukiya kuwa Allah ya mai da Masu mafificiya.
Comments
Post a Comment