Aure Na Daga Cikin Abunda Ke Kawo Zaman Lafiya: Sheikh Bala Lau
Daga Gambo Abubakar Kaduna
Shugaban Kungiyar Jama'atul Izalatul bid'ah wa ikamatus Sunnah a Najeriya, Sheickh Bala Lau ya yi bayanin cewar yawaitar Aure a cikin Al'Umma na daga cikin abunda ke haifar da zama lafiya a kodayaushe.
Aure na sanadiyar kawowa Dan adam natsuwa da tunani mai kyau, wanda hakan na da tasiri ga rayuwa.
Sheikh Bala Lau yayi wannan bayanin ne a yayin wa azin walimar Auren Yayan Karamin Ministan Cikin Gida, kuma tsohon gwamnan Jahar Zamfara Dakta Bello Mohammad Matawalle, su goma a Dakin taro na babban masallacin Juma 'a na kasa da ke Abuja.
Shahararran Malamin addinin musulunci, har ila yau yayi kira ga Karamin Ministan da ya kara damke damtse wajen ganin kawo karshen matsalar tsaro da ta dabaibaye wannan kasa musamman yankin Arewa ma so gabancin kasarnan.
"ina kira ga Malamai da dukkan Jama'ar musulmi da su dukufa da yin addua a wurin Allah da ya yaye mana wannan annoba ta Yan bindiga a wannan yankin namu."
Shugaban jibwis, yayi addua ga shugaban Bola Ahmad Tinubu da Allah ya ba shi ikon yi wa kowa adalci a kasarnan, da samun kwazon kawo karshen matsalolin da ke addabar kasa.
Shi ma a nasa wa'azin, Sheikh Kabiru Haruna Gombe, a kara da cewa Aure ya kunshi Soyayya, Kauna, tausayi, ciyarwa tufatarwa da hayayyafa, wanda dukansu abun so ne ga musulunci.
'rashin yin Aure tamkar nisanta ne daga amfanuwa akan wadannan abubuwa da aka ambata,da falalar da addini ya tanada ga dukkan wanda ya haifi Diya mace yai mata tarbiya har ta girma sannan yai mata Aure, Allah yai mashi alkawalin Aljanna."
A na sa jawabin godiya, Honarabul Bello Mohammed, ya ia hankalin. Alummar musulmi da su dogara da Allah yayin yin aure, ka da su yi tunanin cewar sai sunyi arziki ko sun kai wani matsayi kafin yin Aure.
Tsohon gwamnan Jahar Zamfara, ya nuni da cewar lokacin da ya Auri matansa hudu a lokacin bai da hali kamar yanzu kuma ma bai yi zaton ganin sa a wannan matsayiba.
Tun da darko a nasa jawabin, Tsohon mataimakin gwamnan a Jahar Zamfara, Malam Wakkala Mohammad, yai maraba ga jama ar da su kai tururuwa don ganin wannan hidima, da yin nasiha ga ma aurata da karatun Alqur'ani mai girma.
Sarkin Malaman Gusau, ya gabatar da Kyautar Alqur'anai ga amare don karantashi, da kuma haddarshi a cikin gidajensu, wanda Tsohon gwamnan Jahar Zamfara kuma Marafan Sakkwato Alhaji Abdu"azeez Abubakar Yari ya ba su.
Daga Cikin Malaman da su ka gudanar da nasiha akwai; Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah, da Malam Aminu Aliyu Modibbon Gusau da dai sauransu.
Comments
Post a Comment