KUNGIYAR NPDGGG TA DUKUFA WAJEN SHIRYA ADDU'O'I DON NASARAR MULKIN BOLA TINUBU

Daga Gambo Abubakar Kaduna 

Kungiyar Shirya Addu’oi don samun ingantuwar mulki a karkashin Jam'iyar APC wato (National Prayer Support Group for Good Governance) a Jahar Naija, ta kira ga Jama'ar kasar nan  da su mara mata baya a kokarin ta na shirya taron audu'oi na Kasa da na Jaha da nufin kawo dauki akan matsalolin da su ka dabaibaye kasar  nan.

Kodinatorn kungiyar a Jahar Naija Gimbiya Binta Baba  Gawu, Ita ce ta bayyana hakan yayin da take zantawa da manema labarai a Minna, babban birnin Jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya.

Gimbiya Hajiya Binta Baba ta ce Kungiyar na kokarin ganin ta shirya wannan addu’ar ƙasa ne bisa wasu dakilai da suka zama dole duba da yadda Nijeriya ke fuskantar manyan ƙalubale, ciki har da matsalolin tsaro, tare da neman mafita ga Allah ga shugabanni a kowane mataki.

Gimbiyar ta kara bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan dalilan kafa wannan ƙungiyar addu’a shi ne neman sa hannun Allah, ta hanyar roƙon sa Ya baiwa shugabanni mu ƙarfin guiwa, hikima da ƙarfi domin su isar da kuma aiwatar da ayyukan cigaba da suka sanya a gaba.

A cewarta, matsalolin tsaro da sauran ƙalubalen ƙasa sun kawo cikas a ƙoƙarin shugabanni da suke yi na aiki tukuru domin tabbatar da cewa kowane ɗan ƙasa yana rayuwa cikin zaman lafiya da walwala.

  Binta Gawu  ta kuma yi kira ga al’ummar Jihar Neja da su ci gaba da yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma Gwamnan Jihar Neja, Umar Mohammed Bago, addu’a, inda ta jaddada cewa shugabannin suna ƙoƙarinsu na kawo sauyi mai ma'ana da Samar da walwala a zukatan da kuma fuskokin ‘yan Nijeriya.

A nasa jawabi, babban limamin Masallacin Tunga Central, Sheikh Muhammad Salisu Isah Mai Dalailu, ya yaba da ƙoƙarin Kungiyar Addu’ar, yana mai bayyana cewar addu’a ta a matsayin muhimmin mafita ga matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

Malamin ya Kara da cewar matsalolin tsaro da sauran ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta za su zama tarihi sanu a hankali ta hanyar addu’oi, ya ce Allah Ya yi alkawarin amsa addu’o’in waɗanda suka dage wajen roƙonsa, kuma shi ne ka dai ke iya kawar da dum wars fitina ga Al'umma.

 Shi ma a nasa jawabi, Babban Faston Cocin Redeemed Christian Church of God, kuma memba a cikin ƙungiyar, Pastor Afolabi Kende, ya yaba wa mai kodinatorn bisa ƙoƙarinta na wayar da kan jama’a da kuma nuna kishinta wajan ganin an sami saukin alamura domin shugaban su Sami damar gudanar da ayyukan au na cigaban alumma.

 "Lokacin yayi da dukkan bangaroran addinin musulunci da na kiristiyaniti su had kai don komawa ga Allah wajen neman agajinsa don kawar da matsalolin da su ke addabar kasa."

Haka shima daya daga cikin manyan yan siyasan da suka halarci taron Hassan Musa Zabura ya ce manufar Wannan kungiyar na yin addua zai taimaka wajan kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma Samar da shugabanci na gari da  ci gaban Kasa.

Taron ya samu halartar ‘yan siyasa da shugabannin addinai daga addinai daban-daban, inda dukkaninsu suka haɗu a kan imanin cewa addu’a tana da muhimmanci wajen samun nasarar yaye mahaifa da cigaban ƙasa.

Comments

Popular posts from this blog

Tsafe Development Forum Appeals For An Urgent Support To The Victims Of Bandits Attacks In Chediya Ward

Commander Tradoc Launches 2025 Study Period:- Emphasizes Importance Of Capacity Building

GOV. LAWAL DISTRIBUTES 140 OPERATIONAL VEHICLES TO SECURITY AGENCIES, COMMISSIONS ZAMFARA MASS TRANSIT BUSES