Tinubu Ya Aurar Da Diyan Mininta Matawalle Su Tara A Abuja


Daga Gambo Abubakar
 Kaduna
Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu da takwararsa na Sao' Tome Carlos Bila Boba sun bayar da auran Diyan tsohon gwamnan Jahar Zamfara kuma karmin Ministan tsaro, Bello Mohammad Matawalle, su Tara ga mazajensu.

 Daurin auren wanda ya gudana a babban masallacin Juma'a na kasa da ke Abuja, bayan kammala sallar Juma 'a, ya samu halartar dandazon mutane daga kowanne bangarora na kasar nan.

 Dandazon ma su halarci daurin Auren ya kunshi; takwarorinsa ministoci da gwamnona da tsofafffin gwamnona da kuma kowanne bangaroran Yan  majalisar tarayya, da Yan siyasa Yan kasuwa da Malaman addini.

A nasa tsokaci, shugaban Jam'iyar APC mai kula da yankin Zamfara ta tsakiya a Jahar Zamfara, Alhaji Ahmad Said Mai aya Tsafe, ya bayyana farin Cikin kasamcewar wannan Aure ya Tara mutane daban daban na gida da ketare.

Ma 'ajin Kungiyar ma su sai da Hatsi na kasa, ya baiwa anguna shawarma da su kasamce ma su biyayya ga dokokin Allah a zamantakewar Aure.

Ahmad Mai Aya ya yi kira ga Al'Ummar Jahar Zamfara da su ci gaban da addua akan matsalar tsaro da ta dabaibaye yankin, ya bada tabbacin cewa Allah zai yaye wannan balai, kasamcewar duk abunda yai farko zai shi karshe, akwai sauki bayan wahala.

 Shima  a nasa tsokaci,  tsohon kwamishina na din din din a hukumar zane ta Jahar Zamfara, Sanusi Abdullahi Wanzamai, ya nuna farin Cikin sa yadda ya ga mutane sun yi dandazo a wajen don nuna kara ga Ministan tsaro Bello Mohammad Matawalle.

 Wanzamai ya ba da shawarma anguna da su dauki rigar hakuri, domin hakuri shine ginshikin cin nasarar zamantakewar Aure.

 Ya kuma yi adduar da Allah ya maida kowa lafiya ya ba kowa ladar zumunci ya sa albarka ga wannan hidima.

Comments

Popular posts from this blog

Tsafe Development Forum Appeals For An Urgent Support To The Victims Of Bandits Attacks In Chediya Ward

Commander Tradoc Launches 2025 Study Period:- Emphasizes Importance Of Capacity Building

GOV. LAWAL DISTRIBUTES 140 OPERATIONAL VEHICLES TO SECURITY AGENCIES, COMMISSIONS ZAMFARA MASS TRANSIT BUSES