LIMAN DANBAWA FOUNDATION TA BAYAR DA TALLAFIN KAYAN ABINCI DA KUDI GA MARAYU 120 A GARIN TSAFE


Daga Gambo Abubakar Kaduna 

Gidauniyar tunawa da Liman Mohammad Danbawa dake garin Tsafe ta kaddamar da tallafin Kayan abinci da taimakon kudi ga Marayu har Dari da Ashirin (120), don saukakawa a lokacin Azumi.

 Tallafin wanda ya kunshi kwalin Taliya da kudi Naira Dubu Biyar ga kowanne maraya, wanda ya gudana a harabar gidan Tsohon limamin da ke garin Tsafe.

 A na sa jawabi wajen kaddamar da tallafin, Tsohon kwamishinan lafiya, Alhaji Aliyu Abubakar Mc, Dan masanin Tsafe, ya bayar da tallafin buhun shinkafa da kudi Naira Dubu Hansin ga Malaman Makarantun Allo guda hudu da ke garin Tsafe.

 Makarantu sun hada makarantar Malam Tsalha, Makarantar Malam Haruna, Makarantar Malam Bala mahaddaci da kuma Makarantar Malam Na Baure.
.
 Tsohon shugababn karamar hukumar Tsafe ya kara da cewa, wannan gidauniya ta tallafawa masallacin Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi da sabbin kayan sauti, na kimanin kudi Naira Dubu dari bakwai da Ashirin,(70020,000), kasamcewar shine Masallaci na farko da aka fara da'awar Sunnah a garin Tsafe.

 Har ila yau wannan gidauniya ta ware kudi Naira miliyan biyu da Dubu dari Tara da arbain da daya, (N2,941000) don gyara da sa Solar ga masallacin  Hadejawa, kasamcewar nan ne Liman Danbawa ya fara Tafsiri a cikinsa.

Tsohon zababben dan majalisar tarayya,ya yi nuni da cewar gidauniyar ta kuduri aniyar  kirkiro da hanyoyi don samar da abun dogaro da kai ga Matasan daliban ilimi, da kuma samar da shiri na musamman don neman ma Matasan da ba suyi karatun ba kuma sun tsunduma wajen harkar nanza.

Comments

Popular posts from this blog

Tsafe Development Forum Appeals For An Urgent Support To The Victims Of Bandits Attacks In Chediya Ward

GOV. LAWAL DISTRIBUTES 140 OPERATIONAL VEHICLES TO SECURITY AGENCIES, COMMISSIONS ZAMFARA MASS TRANSIT BUSES

KADUNA CLERGY CALLS ON INCLUSION OF ISLAMIC SCHOOLS INTO NIGERIAN. EDUCATION SYSTEM